Isa ga babban shafi
Yemen-Saudi Arabia

Dakarun kasar Yemen na ci gaba da fatattakar mayakan Huthi mabiya Shi'a

Dakarun masu biyyaya ga shugaban kasar Yemen mai gudun hijira Abdurabbu Mansur Hadi, sun karbe ikon yankunan dake kudancin kasar daga hannun mayakna Huthi mabiya Shi’a, inda kuma suke ci gaba da nausawa zuwa birnin Aden, da shine na 2 mafi girma a kasar.

Sojojin kasar Yemen suna sunturi
Sojojin kasar Yemen suna sunturi REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Garin Zinjibar, da dakarun suka karbe, da shine babban birnin lardin Abyan na hannun dakarun bataliya ta 2 ne, masu biyayya ga hambararren shuigaba Ali Abdullah Saleh, dake baiwa ‘yan tawayen goyon baya.
Wata majiyar sojan kasar tace dakarun sun shiga garin dake gabashin birnin Aden, bayan da suka sha karfin ‘yan tawayen, tare da tallafin hare haren sama daga dakarun kasar Saudi Arabiya.
Jama’ar garin da suka tsere wa fadan, sun fara komawa don garin irin ta’adin da aka yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.