Isa ga babban shafi
Turkiya-ISIS

A na zargin ‘yan jaridun Britaniya da yiwa ISIS leken asiri a Turkiya

Wata kotun Yankin Kurdawan Turkiya ta zargi wasu ‘yan Jaridun Birtaniya biyu da ke aiki wa wani kamfanin Amurka Vice News da laifin yiwa mayakan ISIS leken asiri.

Gangami kan 'yan cin fadin albarkacin baki da aka taba gudanarwa a Turkiya
Gangami kan 'yan cin fadin albarkacin baki da aka taba gudanarwa a Turkiya Reuters/Umit Bektas
Talla

Kanfanin Vice News ya yi watsi da zargin wanda ya bayyana shi a matsayin yunkurin rufe bakin kafofin yada labarai kan abinda ke faruwa a Ynakin.

An dai kama yan jaridun biyu da mai musu fassara da direban su ne, amma daga bisani sai aka saki direban.

Sai dai kotun za ta cigaba da zaman shari'a kan 'yan jaridun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.