Turkiya ta kame mutane 700 ma su son shiga IS
Kasar Turkiyya ta kori mutane sama da 700 a bana ‘yan kasashen waje da suka shiga kasar ko kuma neman tsallakawa zuwa Syria don taimakawa Mayakan IS da ke da’awar Jihadi.
Wallafawa ranar:
Cemalettin Hasimi mai Magana da yawun Firaministan Turkiya ya fadawa manema labarai a birnin Paris a kasar Faransa cewa a bara kawai ma su son shiga 520 aka kama, kuma daga shekara ta 2011 da aka fara yaki a Syria, Turkiya ta kama wadanda ke shirin tafiya Syria akalla 1,800.
Hasimi ya ce hatta ‘yan kungiyar Daesh da na PKK da ke kasar na da hatsari ga Turkiyya.
A cewarsa a kungiyar Daesh a Turkiya na da membobi a kasashe sama da 100, kuma suna ganin muddin aka ci gada da rikici a Syria zata fadada ayyukanta.
Hasimi ya ce suna e bukatar a yi sulhu a kasar Syria domin dakile barazanar ‘Yan ta’adda a Turkiya.
Ya ce Turkiyya na da sunayen ‘yan ta’adda dubu 16,000 da ta haramtawa tsoma kafar su a cikin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu