Isa ga babban shafi
MYANMAR

Shugaban Kasar Myanmar ya gana da 'Yan Tawaye

Shugaban kasar Myanmar Thein Sein a karon farko ya gana da wakilan ‘yan tawaye a wani mataki na kawo karshen rikicin da aka kwashe sama da shekaru Ashirin ana yi, kafin babban zaben kasar a watan Nuwamban wannan shekarar.

Shugaban Kasar Myanmar Thein Sein.
Shugaban Kasar Myanmar Thein Sein. Wikimedia Commons
Talla

Duk da cewa an tashi daga zaman na yau laraba ba tare da nasara ba sai dai an samu ci gaba, ganin kokarin da shugaba Sein ke yi na ganin a biya bukatun bangaren ‘yan tawayen dake ci gaba da fada da dakarun gwamnati.

Shekaru biyu kenan ana tattaunawa domin kawo karshen yakin basasa na tsawon shekaru goma a cikin kasar, amman a yau laraba ne aka kama hanya a taron da ake sa ran zai magance matsalar dake tsakanin gwamnati da musulmai yan kabilar rohingya sai dai kuma wani batu dake kawo cikas shine yadda yan kabilar ta rohingya suka gagara tsayar da wakilai da zasu sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiyar.

Shugaban Sein da ya karbi ragamar mulki shekaru hudu da suka gabata ya sha alwashin samar da zaman lafiya a wannan daddadiyar rikicin da aka kwashe shekaru Ashirin ana yi sakamakon yadda ‘Yan tawaye suka ki amincewa da yadda hukumomi ke nuna wariya da kabilanci a garesu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.