Isa ga babban shafi
Veitnam-Myanmar

Ebola: An kebe wasu ‘Yan Najeriya a Vietnam

Mahukuntan kasar Vietnam da Myanmar sun kebe wasu mutane uku da aka ga alamun suna fama da zazzabi mai nasaba da cutar Ebola bayan sun isa kasashen na kudu maso gabacin Asiya daga Nahiyar Afrika.

Ana tantance Fasinja a birnin Abidjan, kasar Côte d'Ivoire, 13/08/2014
Ana tantance Fasinja a birnin Abidjan, kasar Côte d'Ivoire, 13/08/2014 REUTERS
Talla

Ma’aikatar Lafiya a kasar Veitnam tace wasu ‘Yan Najeriya ne guda biyu aka kebe ana kula da lafiyarsu a wata Asibiti da ke birnin Ho Chi Minh.

Mahukuntan na lafiya sun yi kira ga sauran Fasinjojin da suka shigo jirgi guda da ‘Yan Najeriya daga Qatar zuwa Veitnam akan su zo a diba lafiyarsu.

A kasar Myanmar an kwashi wani mutum zuwa asibitin Yangon daga isowarsa kasar daga kasar Guinea.

Mahukuntan lafiya a Myanmar sun aika jininsa domin gwaji ko yana dauke da cutar Ebola.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin duniya tace cutar ta kashe mutane 84 a cikin kwanaki uku, abinda ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola zuwa 1,229.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.