Isa ga babban shafi
India

Zazzabin Ciwon sauro na hallaka mutane a India

India ta umarci samar da Karin gadaje dubu daya a asibitin birnin Delhi sakamakon sabuwar cutar zazzabin ciwon sauro, mafi muni da ya barke a kasar karon farko a shekaru biyar

REUTERS
Talla

Gwamnatin kasar ta bayyana furgabanta matuka bayan mutuwar wasu Iyayen wani yaro mai shekaru 7, da ya mutu sakamakon zazzabin cizon sauro da ya barke a kasar.

Bayan mutuwar wannan yaro ne dai mahaifinsa da mahaifiyarsa suka kashe kan su saboda bakin cikin abinda ya same dan su.

Sama da mutane 1,714 ne zazzabin ya durkusar a wannan shekarar a kasar, musamman a ‘yan makonin nan.

A cewar Darakatan Ma’aikatar Kiwon Lafiya birnin Delhi YK Mann akwai yiwuwar sake samun yaduwar zazzabin anan gaba lura da halin da ake ciki a yanzu.

Kawo yanzu dai mutane 8  zazzabin ya hallaka
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.