Isa ga babban shafi
Falasdin-Isra'ila

Rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa ya sake tsananta

A na ci gaba da samun tashin hankali tsakanin Isra’ila da mazauna gabar yammacin kogin Jordan, inda a halin yanzu rahotanni ke cewa an hallaka wasu mutane 3 da Jami’in dan sanda 1, a dai-dai lokacin da shugabanni Falasdinawa da Isra’ila ke kokarin kwantar da tarzomar.

Rikicin Falasdinawa da Isra'ila a yammacin Kogin Jordan
Rikicin Falasdinawa da Isra'ila a yammacin Kogin Jordan Reuters/路透社
Talla

Rahotanni sunce Jami’an tsaron Isra’ila sun bude wuta kan Falasdinawa da ke jifansu da duwatsu abin da ya hadasa jikata 3 daga cikinsu.

Falasdinawa dai na yawaita zargin Isra’ila da amfani da masu jin harshan larabci wajen ingiza zanga-zanga.

A wasu yankuna kuma irin su Kiryat Gat da ke tsakiyar Isra'ila, 'Yan sanda sun harbe wani balarabe har lahira bayan sokawa wani soja wuka tare da kwace bindigar sojin.

Wannan tashin hankali ya sanya Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu dage tafiyar da yake shirin kaiwa zuwa Jamus a gobe Alhamis domin neman hanyar lafar da kura fittinar da ke neman zarce mako 3 duk da kiraye-kirayen da akeyi musu na zaman lafiya.

Ko a ranar Talata data gabata sai da Jami’an tsaron bangarorin 2 da ke rikici suka gana bayan Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya ce baya son rikicin ya zafafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.