Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Shirin Nukiliyar Iran ya samu amincewar Karshe

Yarjejeniyar Shirin Nukiliyar Iran da kasashen duniya ya samu amincewar karshe daga Majalisar malaman Juyin juya halin Kasar, bayan Jefa Kuri’ar tabbatar da cewa shirin bai sabawa Kudin tsarin mulkin kasa ko dokokin Addini Musulci ba.

Shugaban Juyin Juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei
Shugaban Juyin Juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei AFP PHOTO / HO / KHAMENEI.IR
Talla

Amincewar Majalisar ya biyo bayan gudanar da Muhawara da kada kuri’u kan dokokin da Iran da kasashen duniya suka cimma kafin kulla wannan Yarjejeniyar, wanda aka jima ana kai wa da komo wa Musamman tsakanin Kasar da Amurka.

A tarihi akwai da daddiyar takun saka tsakanin ‘Yan Majalisun dokokin Amurka da na Iran, tun lokacin Juyin Juya halin shekarar 1979.

Shirin dai a yanzu zai bayar da daman dage wa Iran takunkumi, bayan Iran ta tabbatar da cewa shirin Nukiliyarta na zaman lafiya ne.

A watan satumba da ya gabata ‘Yan majalisun Amurka suka gagara dai-daita kansu domin baiwa Shugaban Kasar Barack Obama cikakken goyon baya Kan wannan shiri.

Ita dai Iran bukatar ta itace a dage mata takunkumi zuwa karshan shekarar na ko farkon watan Janairun badi.

Sai dai a yanzu ya zama dole Iran ta tabbatar wa Hukumar kula da makamashin Nukiliya ta duniya na Majalisar Dinkin Duniya yanayi yadda za ta gudanar da shirin ba tare da cutarwa ba.

Ranar 15 ga watan Disamba shine ranar karshe da aka baiwa Iran domin kare kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.