Isa ga babban shafi
MDD

Isra'ila za ta hana Iran mallakar nukliya

Firaministan Isra’ila Benjamin Netenyahu wanda ya gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar alhamis, ya ce kasar za ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiya ba.

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu a yayin gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu a yayin gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya. REUTERS/Andrew Kelly
Talla

Benyamin Netenyahu ya shaida wa taron zauren Majalisr Dinkin Duniya cewa Isra’ila ba za ta yarda wata kasa a duniya ta kasance barazana ga makomarta ba, yana mai yin kakkausar suka a game da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Iran da kasashen duniya kan shirin nukiliya.

Yarjejejeniyar kamar dai yadda Netenyahu ya ci gaba da cewa a jawabin nasa, ba abinda za ta haifar face share wa Iran fage domin mallakar makaman nukiliya, kuma hakan barazana ce ga zaman lafiyar duniya.

Tun lokacin da aka kulla wannan yarjejeniyar ce dai Isra’ila ta fito fili ta nuna rashin amincewa da ita, inda a maimakon samar da zaman lafiya, Benyamin Netenyahu ke cewa za ta haifar da sabon rikici ne musamman a tsakanin kasashen yankin gabas ta tsakiya.

To sai dai a wani bangare na jawabinsa, Firaministan na Isra’ila ya ce a shirye yake ya koma teburin tattaunawa da hukumomin Palasdinu ba tare da ya gindaya wani sharadi ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.