Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta soki manyan kasashen yammaci kan batun Nukiliya

Iran da manyan kasashen yammaci sun tashi baran-baran ba tare da sun cim ma yarjejeniya ba a jiya Alhamis a birnin Vienna, yayin da bangarorin biyu suka samu sabani kan bukatun da ke gaban yarjejeniyar harmatawa Iran mallakar makaman nukiliya.

Javad Zarif da Jami'an Diflomasiyar Iran.
Javad Zarif da Jami'an Diflomasiyar Iran. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Iran ta zargi manyan kasashen na yammaci da komawa kan bukatun da ke cikin yarjejeniyar da suka amince a watan Afrilu, lamarin da ya sa bangarorin biyu suka tashi baran-baran ba tare da cim ma yarjejeniyar ba a jiya Alhamis.

An shafe kwanaki 13 Iran da manyan kasashen duniya guda 6 na tattauna batun nukiliyar kasar.

Wakilan Iran a zauren tattaunawar sun ki amincewa da bukatun kasashen na yammaci bayan sun koma ga kudirorin da ke cikin yarjejeniyar watan Afrliu.

Manyan kasashen guda 6 da suka hada da Amurka da Faransa da Birtaniya da China da Rasha da kuma Jamus na son janyewa Iran jerin takunkuman da suka kakaba ma ta domin ta jingine ayyukanta na mallakar makaman Nukiliya.

Babu tabbas yanzu ko manyan kasashen za su amince da bukatun Iran da ta dade tana ikirarin shirinta na inganta makamashi ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.