Isa ga babban shafi
MDD-Isra'ila-Falasdinu

Ban ya ja kunna Isra'ila da Falasdinu kan zaman lafiya

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira ga Yahudawan Isra’ila da kuma Falasdinawa su kawo karshen rikici tsakaninsu bayan shafe makwanni uku suna kisan juna.

Sakatare Janar na MDD  Ban Ki-moon
Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon REUTERS/Darren Ornitz
Talla

Mr Ban ya yi wannan kiran ne a wata ziyarar ba-zata da ya kai a birnin Kudus da kuma yankin Falasdinawa a yau Talata.

Ban wanda ya fara jawabinsa cikin Salama, ya gargadi cewa rikici na iya haifar da Baraka ga kokarin Falasdinawa na samun yancin cin gashin kai da kuma cigaba da haifar da barazanar ga tsaron Isra’ila.

Ban Ya ce , ya fahimci halin da matasan Falasdinawa suke ciki, Musamman batun yancinsu na tafiyar da al’amuransu cikin girmamawa.

A karshe Mr. Ban ya jadada cewa tabbas ya san cewa wannan shi ne muradin Falasdinawa amma kuma suna iya cimma wannan bukatar, idan suka samar da hurumin wanzar da zaman lafiya tsakaninku da Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.