Isa ga babban shafi
Amurka-Isra'ila-Falasdinu

Kerry ya gana da Netanyahu kan zaman Lafiya a Kudus

Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry ya bukaci Isra’ila da Falasdinawa da su kauracewa duk wani abu da ka iya hura wutar rikici tsakaninsu, domin samar da zaman lafiya a tsakaninsu.Kiran kerry na zuwa ne, a ganawarsa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netenyahu a Berlin.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ganawarsu da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a Berlin
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ganawarsu da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a Berlin REUTERS/Carlo Allegri
Talla

A ganawar da suka yi na Sa’o’i 4, Netanyahu ya ce Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, da kungiyar Hamas, suke ingiza hare-haren da Falasdinawa suka rika kaiwa da wuka a kan Isra'ilawa a 'yan kwanakin nan.

Sai dai kuma Kerry ya ce akwai abubuwa da ake da bukatar gindayawa domin shawo kan wannan matsala a cikin gaggawa.

Kerry wanda ya zanta da Netanyahu kan batutuwa da dama, ya ce akwai bukatar tattaunawa da Abbas da sarkin Jordan kan hanyar ware-ware wannan rikici.

A tashe-tashen hankula tsakanin isra’ila da Falasdinu ko a baya-baya nan, dan Isra'ila ya ji mummunan rauni bayan da wasu Falasdinawa suka caccaka masa wuka a birnin Kudus.

‘Yayin da suma wasu sojoji suka bindige wani dalibi Bayahude bayan sun yi zaton cewa wani Bafalasdine ne zai kai hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.