Isa ga babban shafi
Faransa-Syria

Wani Bam da jirgin yakin Faransa ya harba a Raqa ya gagara fashewa

Rundunar sojan Faransa ta ce, wani Bam daga cikin Bama-bamai sama da 60 da jiragen yakin Faransa suka jefa a makon da ya gabata a garin Raqa tingar mayakan jihadin kungiyar ISIS a kasar Syriya ya ki fashewa, sai dai kuma ba zai taba sake yin fanni ba nan gaba.

Wani bam  din jirgin yakin kasar Rasha
Wani bam din jirgin yakin kasar Rasha
Talla

Kawo yanzu dai kasar Faransa ta kai hare hare 3 a kan wurare masu muhimmanci na mayakan jihadin dake Raqa cikin kasar Syria, a matsayin maida martani kan harin ta’addancin birnin Paris.

A lokacin wani taron manema ne a yau alhamis a birnin Paris, kakakin rundunar sojan Faransa colonel Gilles Jaron ya ce, a bayanan da suka samu, sun bayyana masu cewa, daya daga cikin jerin bamabaman da suka jefa bai tarwatse ba.

Sai dai kuma hafsan sojan ya kara da cewa, sakamakon haduwa da doron kasa da karfi, Bom din ba zai saake yi amfani ba ta mahangar aikin soja, ma’ana ba za a iya sake makala shi a jirgi a harba ya tashi ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.