Isa ga babban shafi
Faransa-Rasha

Faransa da Rasha sun zafafa hare-hare a Syria

Dakarun kasar Faransa da na kasar Russia na ta zafafa hare-hare kan mabuyar kungiyar ISIS, masu ikirarin jihadi a Syria inda a yau kawai aka kashe mutane 33 a yankin Raqa.

Jiragen Yakin Rasha a Syria
Jiragen Yakin Rasha a Syria Reuters/路透社
Talla

Harin yau na zuwa ne kwana daya bayan da Rasha ta ce jirgin saman fasinjanta daya fadi kwanan baya a yankin kasar Masar har mutane 224 suka mutu, ‘yan taadda ne suka tarwatsa mata shi da bam.

Kungiyar masu jihadin ta IS dai sun dau alhakin hatsrain jirgin na Rasha da kuma harin da aka kai Paris na Faransa karshen makon daya gabata inda mutane 130 suka mutu.

Daga lahadi da ta gabata zuwa yau Laraba, hare-haren da Rasha da Faransa ke ta kaiwa Syria sun lalata wurare da dama, da suka hada da inda kungiyar IS ke tara makamanta, da barikin da mayakan ta ke zaune a birnin Raqa.

Ministan tsaro na Faransa Jean-Yves Le Drain ya bayyana cewa matakin da suka dauka ya dace.

Wasu alkalumma da kungiyoyin dake sa idanu kan rikicin Syria suka gabatar na nuna cewa cikin kwanaki 3 mutane masu yawan gaske aka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.