Isa ga babban shafi
Amurka

Wasu Jihohin Amurka sun daina karbar ‘Yan Syria

Wasu daga Jihohin kasar Amurka sun sanar da dakatar da karbar ‘Yan gudun hijira da ke fitowa daga kasar Syria saboda abin da suka kira fargaba bayan samun fasfo din dan kasar kusa da daya daga cikin wadanda suka kai munanan hare hare a Paris.

'Yan Gudun hijira da ke neman mafaka a Faransa
'Yan Gudun hijira da ke neman mafaka a Faransa REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Gwamnan Michigan Rick Snyder ya sanar da dakatar da karbar sabbin ‘Yan gudun hijira da ke shigowa Amurka, kuma matakin ya samu goyan bayan Jihohin Alabama da Texas da wasu jihohin kasar.

Shugaba Barack Obama ya bukaci Amurka ta bude kofarta ga masu tserewa yakin da ake yi a Syria, yana mai cewa rufe kofa tamkar cin amanarsu ne.

Hare haren da akai a Paris a ranar Juma’a ya razana kasashen yammaci da ke karbar Miliyoyan ‘Yan gudun hijirar Syria da ke kauracewa rikicin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.