An kona runfunar ‘Yan gudun hijira a Sweden
Rahotanni daga kasar Sweden sun ce an kona wasu runfunan da gwamnatin kasar ta kafa da nufin karbar baki ‘Yan gudun hijira a yau Assabar. ‘Yan sanda a kasar sun ce da gangan aka cinna wa runfunar wuta a garin Floda da ke kudu maso yammacin kasar.
Wallafawa ranar:
Zuwa yanzu dai babu labarin ko gobarar ta haifar da wani ta’adi na mutuwa ko rauni sannan babu wanda ‘Yandan kasar suka cafke.
An kiyasta cewa Sweden ta karbi baki ‘Yan gudun hijira kusan 200,000 a bana amma a ranar Alhamis gwamnatin kasar tace zata daina karbar ‘yan gudun hijirar wadanda ke ci gaba da kwarara zuwa kasashen Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu