Isa ga babban shafi
Yemen

Bangarorin da ke rikici da Juna a Yemen sun amince da zaman sulhu

Gwamnatin Yemen tare da wakilan ‘yan tawayen kasar sun amince zasu halarci taron sulhu da za ayi a kasar Switzerland a gobe Talata karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya da niyar kawo karshen yakin da ake yi a kasar.

Shugaban Kasar Yemen Abderrabbu Mansur Hadi
Shugaban Kasar Yemen Abderrabbu Mansur Hadi REUTERS/Stringer
Talla

Sanarwar taron sulhun na zuwa ne a yayin da gwamnatin kasar Yemen ke cewa wani kwamandar sojin Saudiya ya rasa ransa a wani harin sama da aka kai a kasar ta Yemen.

Sai dai duk da haka an bukaci zaman sulhu don ganin an dakatar da rikicin kasar ganin kusan kashi 80 cikin 100 na al’ummar kasar ke bukatan taimako na kayyakin agaji.

Kawo yanzu ma dai bangarorin biyu basu fitar da wata sanarwar da ke nuna cewa suna da niyar halartar taron ba duk da cewa sun ce akwai bukatar tsagaita wuta a rikicin kamar yadda wakilin MDD a taron da aka yi a birnin Riyadh a makon da ya gabata ke cewa.

Sama da shekara daya kenan ‘yan tawayen suka kama birnin Sanaa da har yanzu suke ta fafatawa.

A watan uku wannan shekarar Kungiyar Kasashen Larabawa suka shiga cikin fadan don goyon bayan shugaban kasar Abdelrabbo Mansour Hadi amma kuma har yanzu sun kasa warware rikicin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane akalla 5,800 ne suka gamu da ajalinsu tun barkewar rikicin kasar, yayin da fiye da miliyan daya suka resa matsugunninsu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.