Amnesty ta zargi Rasha da kashe fararen hula a Syria
Kungiyar Amnesty International ta zargi Rasha da kashe daruruwan fararen hula a hare haren saman da ta ke kai wa a Syria, inda ta ce hakan na iya zama laifukan yaki.
Wallafawa ranar:
Philip Luther, daraktan kungiyar da ke kula da yankin Gabas Ta Tsakiya da Arewacin Afrika ya ce, wasu hare haren ana kai su ne kawai kan fararen hula ko kuma gidajen jama’a da asibitoci.
Kungiyar ta ce binciken da ta yi ya nuna cewa, a cikin watanni uku da fara kai hare haren biranen Homs da Idlib da Aleppo, Rasha ta hallaka fararen hula sama da 200
Rasha dai ta ce tana kaddamar da farmaki ne kan 'yan ta'adda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu