Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta harbo jirgin Rasha a Syria

Turkiya ta kakkabo wani jirgin yakin Rasha akan iyakar Syria a yau Talata, a wani mataki da ake ganin zai kara haifar da tankiya tsakanin kasashen biyu da ke da sabanin ra’ayi a rikicin kasar Syria.

Hutunan Telebijin sun nuna yadda jirgin Rasha ke cin wuta a samaniya wanda Turkiya ta harbo
Hutunan Telebijin sun nuna yadda jirgin Rasha ke cin wuta a samaniya wanda Turkiya ta harbo REUTERS/Reuters TV/Haberturk TVATTENTION EDITORS
Talla

Ma’aikatar tsaron Turkiya tace wasu jiragenta biyu ne suka harbo jirgin, bayan ya sabawa dokokin sararin samaniyarta kusan sau 10 cikin mintina 5.

Kuma kafofin yada labaran Turkiya sun ruwaito cewa an cafke daya daga cikin matukin jirgin bayan ya dire kasa daga jirgin a parachute, yayin da kuma wasu rahotanni ke cewa matukin guda ya mutu daya kuma ya bata bayan harbo jirgin.

Rasha ta karyata ikirarin jirginta ya ratso ta Turkiya ne daga Syria, bayan ta yi allawadai da harbo shi.

Hutunan Telebijin sun nuna yadda jirgin ya ke cin wuta a samaniya da yadda ya tarwatse akan tsauni a yankin kan iyakar Syria.

Tuni dai aka yi fargabar aukuwar irin haka saboda Kasancewar jiragen Rasha da Faransa da Amurka da Turkiya da wasu kasashen larabawa a Syria.

Kuma yanzu ana ganin wannan zai kara haifar da rashin fahimtar juna tsakanin Rasha da Turkiya da ke da sabanin ra’ayi akan rikicin Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.