Isa ga babban shafi
Russia-Masar

Da bam aka tarwatsa jirgin mu a Masar inji Rasha

A karo na farko a yau talata, kasar Rasha ta tabbatar da cewa fashewar bam ce ta yi sanadiyar hatsarin jirginta a Masar inda tayi alkawarin gano wadanda ke da hannu a wajen kai harin, tare da kara yawaita hare-haren jiragen saman yakinta a kasar Syria.

Yankin da Jirgin Rasha ya yi hatsari a Masar
Yankin da Jirgin Rasha ya yi hatsari a Masar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Makwanni 2 bayan aukuwar hadarin jirgin saman kasar Rasha da ya tarwatse a sararin samaniyar yankin Sinai na kasar Masar dauke da fasinjoji 224.

A cikin wata Sanarwa data fitar Ma’aikatar leken asirin kasar Rasha FSB ta yi tayin bada tukuicin miliyan 50 na dalar Amurka, ga duk mutumin da ya taimaka ya bada labarin yan ta’addan da suka kai harin.

A lokacin wani zaman taro a fadar Kremlin, da ya hada shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin, da shugaban hukumar leken asirin kasar Alexandre Bortnikov, sun danganta hatsarin jirgin fasinjar samfarin A321 a yankin tsaunukan Sinai na kasar Masar da zama na ta’addanci

Shugaban hukumar leken asirin ta FSB M. Borotnikov, ya ce, bam din na gargajiya mai karfin kilogram na TNT ya tarwatse ne a lokacin da jirgin ke tsakkiyar keta hazon sararin samaniya yankin na Sinai.

Tun da farko dai kasashen Amurka da Britaniya sun bayyana hasashen cewa Bam ne ya haddasa hadarin.

Sai dai kuma a nata bangaren kasar Masar ta bakin ministan dake kula da filayen jiragen saman fararan hula Hossam Kamal ta kafar TV din kasar ya ce har yanzu ba a kammala binciken da ake yi ba, a kan gano musabbabin abinda ya hadassa hatsarin da tuni kungiyar mayakan ISIS ta ce ita ta kakkabo jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.