Hadarin Jirgi: Rasha da Masar sun musanta ikirarin IS
Kasashen Rasha da Masar sun yi watsi da ikirarin kungiyar nan mai da’awar kafa daular musulunci wato IS da ke cewa mayakanta ne suka harbo jirgin Rasha dauke da mutane 224 da ya yi hatsari a yankin Sinai na Masar.
Wallafawa ranar:
Tuni dai Rasha ta sanar da zaman makoki tare da yin kasa da tutocinta, domin alhini dangane da hasaran rayukan da aka samu a hadarin yayin da kwararru ke kan gudanar da bincike domin gano dalilin faruwar lamarin.
A jiya ne dai jirgin ya taso daga wurin shaktatawa na Sharm el-Sheik da ke masar da nufin zuwa birnin saint Petersburg na Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu