Isa ga babban shafi
Masar

Jirgin Rasha ya tarwatse ne a sama-Kwararru

Kwararru sun bayyana cewa jirgin saman Rasha da ya yi hatsari a yankin Sinai na Masar, ya samu matsala ne a sararin samaniya, inda sassan jikinsa suka tarwatse.

Matane 224 suka rasu a hadarin jirgin na Rasha
Matane 224 suka rasu a hadarin jirgin na Rasha REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Kwamitin kula da zirgar zirgar jiragen Sama na kasa da kasa a Rasha, ya bayyana cewa sassan jirgin sun tarwatse ne a sararin samaniya kuma sun bazu a wani yankin mai girman gaske.

To sai shugaban kwamitin masu bincike kan dalilin faruwan hatsarin, Victo Sorochenko ya bayyana cewa ya yi wuri a iya gano musabbabin hadarin jirgin wanda ya yi sanadiyar mutuwar ilahirin mutane 224 da ke cikin sa.

Masu bincike dai sun gano bakin akwatin jirgin kuma gwamnatin Masar ta ce ana ci gaba da tattance bayanan da akwatin ya nada.

Shugaban Masar Abdel Fatah al-Sisi ya bukaci a kwantar da hanlaki har a gano musabbabin wannan mummunan hatsarin da kungiyar IS ta yi ikirarin cewa ita ta haifar da shi bayan ta kakkabo jirgin a yankin Sinai da ke Masar amma hukumomin Rasha da Masar sun yi watsi da ikirarin kungiyar.

Kawo yanzu dai an yi nasarar gano gawarwaki 168 da ya hada da gawar wata yarinya da aka tsinta a can wani yanki mai nisan kilomita takwas daga inda aka samu akasarin buraguzan jirgin.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.