Isa ga babban shafi

Cin zarafin mata ya ta'azzara a ƙasashe masu fama da rikici a 2023 - MDD

Majalisar Dinkin Duniya  ta ce cin zarafi ta hanyar jima'i da ke da nasaba da rikice-rikice ya tsananta a shekarar 2023 da ya gabata masamman ga mata.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin zantawa da manema labarai a New York na kasar Amurka.8/11/2023
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin zantawa da manema labarai a New York na kasar Amurka.8/11/2023 © Brendan McDermid / Reuters
Talla

Cikin rahotan Majalisar Dinkin Duniya na ranar Jumma’a, Sakatare Janar na Majalisar, Antonio Guterres, ya ce ƙasashe masu fama da rikici na amfani da cin zarafi kamar su Fyade tilasta karuwanci da auren dole a matsayin dabarun yaki.

Guterres ya yi kalamun ne a bitar halin da ake ciki a Afganistan da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Burma da Sudan da Mali har ma da Haiti inda ƙungiyoyin ‘yan daba ke yin lalata mata.

Wuraren tsare mutane

Wadanda abin ya shafa mafi akasari mata da ‘yan mata da kuma tsirarun maza da samari har ma da wadanda sauya jinsi, sun fi fuskantar cin zarafi ne a wuraren da ake tsare da su. Misalin yammacin kogin Jordan, wanda ya raba Isra'ila da yankunan Falasdinawa: Bayanan Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar da rahotanni game da kame tare da tsare mata da maza Falasdinawa da jami'an tsaron Isra'ila suka yi bayan Hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba, galibi suna fuskantar azabtwarwa tare da duka, da cin zarafi da wulakanci, da suka hada da cin zarafi, kamar harbin al’aura da barazanar fyade. rahotan ya kuma ambaci abin tashin hankalin da sojojin Isra'ila suka aikata a Gaza bayan kaddamar da farmaki ta ƙasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.