Afghanistan
Girgizan kasa ta abkawa Afghanistan
Girgizan kasa mai karfin maki 6.2 ta abkawa arewa maso gabashin kasar Afghanistan kusa da kan iyaka da Pakistan da Tajikistan, kuma rahotanni sun ce akalla mutane 30 suka samu rauni.
Wallafawa ranar:
Talla
Girgizan kasar dai ta razana mazauna Kabul a Afghanistan da kuma mutanen Islamabad a Pakistan bayan gidaje sun fara girgiza.
A watan Oktoba wata girgizan kasa mai karfin maki 7.5 da ta abkawa Afghanistan da Pakistan ta kashe mutane kusan 400 tare da rusa gidaje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu