Syria
An kashe wani kwamandan ‘Yan tawayen Syria
An kashe wani babban kwamandan ‘Yan tawayen Syria Zahran Alloush a wani harin sama da gwamnarin kasar ta kai a gabashin Ghauta a jiya Juma’a.
Wallafawa ranar:
Talla
An bayyana Alloush a matsayin kwamandan kungiyar Jaish Al-Islam daya daga cikin kungiyar ‘Yan tawayen Syria a gabashin Damascus. Kuma an kashe shi ne tare da wasu mayakansa guda 5.
Kungiyar da ke sa idanu ga rikicin Syria tace kungiyar ta nada sabon shugaba Abu Himam al Buwaydani bayan kisan Allaoush.
Amma aAna tababa akan ko jiragen yakin Syria ne ko na Rasha suka kashe kwamandan na ‘Yan tawaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu