Isa ga babban shafi
IRAN-SAUDIA

Iran ba ta da niyyar shiga yaki da kasar Saudiyya

Iran ta ce ba ta da niyyar fafatawa a fagen yaki tsakaninta da Saudiyya, a daidai lokacin da kasashen biyu ke ci gaba da kai ruwa rana sakamakon kashe wani malamin Shi’a da Saudiyya ta yi.

Ministan wajen Iran, Mohammad Javad Zarif
Ministan wajen Iran, Mohammad Javad Zarif REUTERS/Raheb Homavandi/TIMA
Talla

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Javad Zarif ya bayyana wa taron tattalin arzikin duniyar da ake yi a Davos da ke kasar Switzerland cewa, bai kamata a yi tunanin faruwar yaki a tsakanin kasashen biyu ba.

Ministan ya ce Iran ba ta yi wa wata kasa barazana, kuma a shirye take ta tattauna da makwabtanta domin fahimtar juna.

Takaddama tsakanin kasashen biyu ta yi tsami sakamakon kashe Sheikh Nimr al Nimr da Saudiyya ta yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.