ISIS ta kashe mutane fiye da 100 a Syria
Akalla mutane 101 ne suka rasa rayukansu sakamakon munanan hare haren da kungiyar ISIS ta kaddamar a sansanonin sojojin Syria a wannan Litinin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a Syria ta ce, mayakan sun kai harin farko a birnn Jableh, inda nan take suka kashe mutane 53 yayin da hari na biyu da aka kai a birnin Tartus ya lakume rayuka 48.
Rahotanni sun ce, wannan dai, shi ne farmaki mafi muni da aka kai a biranen tun bayan da Syria ta fada cikin rikici a shekara ta 2011.
Jim kadan da aukuwar lamarin ne, kungiyar ISIS mai da’awar jihadi ta sanar da daukan alhakin hare haren na kunar bakin wake.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu