Isa ga babban shafi
Iraqi

Fararen hula sun samu hanyar ficewa Fallujah

Rundunar Sojin kasar Iraqi ta samar da hanyar ficewa daga birnin Fallujah wanda ya bai wa fararen hula kusan 4,000 damar tserewa cikin sa’o’I 24 daga garin da mayakan IS suka kwace.

Fararen hula na ficewa Fallujah.
Fararen hula na ficewa Fallujah. Reuters
Talla

Kungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta Norway ce ta sanar da matakin, bayan IS ta kashe mutane 18 iyalan gida biyu ranar juma’a.

Rundunar sojin Iraqi ta kara kaimi don karbe ikon garin daga mayakan.

Kimanin mutane 24,000 suka fice Fallujah tun lokacin da dakarun Iraqi suka kaddamar da farmakin kwato garin daga IS a 22 ga watan Mayu.

Sai dai kuma akwai fararen hulda da dama da suka makale a tsakiyar Fallujah inda mayakan IS ke yin garkuwar yaki da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.