Isa ga babban shafi
Indonesia

An harbe 'yan Najeriya 3 a Indonesia

Gwamnatin Kasar Indonesia tayi watsi da kiraye kirayen da Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar kasashen Turai da kungiyoyi kare hakkin Bil Adama suka mata na dakatar da aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutane 14 da aka samu da laifin safarar kwayoyi a kasar.

Wasu daga cikin wadanda aka zartas da hukuncin kisa a kansu saboda safarar kwayoyi a Indonesia
Wasu daga cikin wadanda aka zartas da hukuncin kisa a kansu saboda safarar kwayoyi a Indonesia REUTERS/Beawiharta
Talla

A daren jiya, hukumomin kasar sun harbe 4 daga cikin mutane 14 da aka yankewa hukunci a wani tsibiri dake teku, cikin su harda 'Yan Najeriya guda 3.

Ana saran kashe sauran 10 a karshen wannan mako.

Kafewar Indonisian kan zartar da hukuncin kisan na zuwa ne bayan da jami-an kare hakkin bil-adama na majalisar Majalisar dinkin duniya suka bukaci kasar ta sake shawara game da aniyarta.

Babban jami-in kare hakkin bil-adama na majalisar Zied Ra-ad al-Hussain ya bayyana yawaitar zaratar da hukuncin kisa a kasar ta Indonesia a matsayin abin da ya sabawa yancin dan adam.

Ra-ad al-Hussain yace hukuncin kisan ba ya tasiri wajen rage laifukan tu-ammuli da miyagun kwayoyi bale kuma ya kai ga kare mutane fada wa laifin.

Shugaban kasar Indonesia, Joko Widodo, ya sha kare matsayin kasar game da zartar da hukucin kisa ga masu safara ko shan kwayoyi, da cewa, alkalumma sun nuna a kalla 'yan kasarsa 50 ke mutuwa a kowa ce rana dalilin tu-ammali da kwayoyin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.