Isa ga babban shafi
Syria

Mutane 500 sun mutu cikin mako guda a Syria

Kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a Syria ta ce, fiye da ‘yan tawaye da dakarun gwamnatin kasar 500 ne suka rasa rayukansu a cikin mako guda da aka shafe ana gwabza yaki da nufin karbe birnin Aleppo daga hannun mayakan jihadi.

Fiye da mutane 500 sun mutu a yakin mako guda a Aleppo na kasar Syria
Fiye da mutane 500 sun mutu a yakin mako guda a Aleppo na kasar Syria REUTERS/Abdalrhman Ismail
Talla

Shugaban kungiyar Rami Abdel Rahman ya bayyna cewa, akalla fafaren hula 130 ne suma suka mutu sakamakon farmakin da ‘yan tawayen suka kaddamar a yankunan da dakarun gwamnati ke rike da su.

A bangare guda, ‘yan tawayen na Syria sun ce, sun wargaza kawanyar makwanni uku  da dakarun gwamnatin suka yi musu a birnin na Aleppo, lamarin da ya dagule ayyukan dakarun da ke samun goyon bayan Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.