Isa ga babban shafi
Asiya

An kame mayakan ISIS a Malaysia

Jami'an tsaro kasar Malaysia sun kame mutane 9 da ake zargin ‘yan kungiyar ISIS ne.

Prime Ministan Malaysia Najib Razak
Prime Ministan Malaysia Najib Razak REUTERS/Lai Seng Sin
Talla

Sati biyu da suka gabata ne hukumar ‘yan sandan Malaysia suka kaddamar da sumamen zakulo ‘ya’yan kungiyar ISIS a kasar.

Sifeto Janar din ‘yan sandan kasar Khalid Abubakar ya ce daga cikin wadanda aka kama akwai mutum biyu da suka kai harin gurneti a wata mashaya a Kuala Lumpur a watan Yunin da ya gabata.

Bayan kai harin a mashayar, wani jagoran ISIS a Syria ya dauki alhakin shirya kai harin, wanda ya zama na farko da mayakan suka kai a kasar Malaysia.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.