Isa ga babban shafi
Malaysia-Ukraine-Rasha

BINCIKE:Da makami mai Linzami aka harbo Jirgin Malaysia MH17

Masu binciken hatsarin Jirgin Malaysia Samfurin MH17 da ya kashe mutane kusan 300 sun fito da sakamakon bincikensu na Karshe, inda suka tabbatar da cewa harbo jirgin aka yi daga gabashin Ukraine da Makami mai Linzami BUK da Rasha ke kerawa.

Tarkacen Jirgin Malaysia MH17 da aka tsinto
Tarkacen Jirgin Malaysia MH17 da aka tsinto REUTERS/Maxim Zmeyev
Talla

Hatsarin wannan jirgi a bara ya kasance irin sa na farko a tarihi safaran jiragen sama baya jirgin MH370 na Malaysia da ya yi batan dabo dauke da Fasonjoji sama da 200 a watan maris din bara.

Shugaban Tawagar Masu binciken daga kasar Nerthaland Tjibbe Joustra ya ce mafi yawan tarkacen Jirgin Samfurin MH17 an tsinto su ne a kauyuka da dama da suka hada da Grabove, Rozsypne da Ptropavlivka da ‘yan tawayen ukraine suka fi yawa.

Bincike ya kuma tabbatar da cewar an harba makamin mai linzami ne daga nisa kilomita 320 daga gabashin Ukraine.

Malaysia dai ta sha alwashin shigar da karar wadan da ke da alhakin rikitowar wannan jirgi.

Rasha dai ta bayyana shakun ta dangane da wannan Sakamako.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.