Isa ga babban shafi
Afghanistan

'Yan bindiga sun harbe mutune 12

Jami'an tsaro sun ce mutane 12 daga ciki dalibai bakwai ne suka rasa rayukansu yayin harin da 'yan bindiga suka kai kan wata Jami'ar kasar Amurka a Kabul babban birnin kasar Afghanistan.  

Ana kula da wadanda suka samu raunuka a harin Jami'ar Amurka a Kabul
Ana kula da wadanda suka samu raunuka a harin Jami'ar Amurka a Kabul REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Jam’in tsaro da fari sun yi wa ginin Jami'ar kawanya kafin daga bisani su kutsa ciki tare da samun nasarar kashe 'yan bindigar guda biyu.

Shugaban 'yan sanda a Kabul Abdul Rahman Rahimi ya ce wadanda suka rasa rayukansu sun hada da dalibai bakwai, 'yan sanda uku, da kuma masu gadi biyu.

Harin yazo sati biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka sace malamai biyu na Jami’ar Amurkan da ke Kabul, daya dan kasar Australia dayan kuma dan Amurka, har yanzu kuma babu labarinsu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.