Isa ga babban shafi
Afghanistan

An kai hari kan 'yan yawon bude ido a Afghanistan

Kungiyar Taliban ta kai hari kan ayarin masu yawon bude ido da ke samun rakiyar sojoji a yammacin lardin Harat da ke kasar Afghanistan, inda mutane shida suka jikkata.

An tarwatsa mayakan Taliban da suka kaddamar da hari kan baki masu yawon bude ido a Afghanistan
An tarwatsa mayakan Taliban da suka kaddamar da hari kan baki masu yawon bude ido a Afghanistan REUTERS/Stringer
Talla

Kawo yanzu ba a sanar da asalin kasashen masu yawon bude idon ba, yayin da mai magana da yawun gwamnan Heart ya ce, harin kwantan bauna aka kai wa ayarin.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Najibullah Najibi ya ce, tuni jami’an tsaro suka tarwatsa mayakan na Taliban, inda kuma aka yi wa bakin rakiya zuwa tsakiyar birnin Herat.

Harin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar Taliban ta zafafa kaddamar da farmaki bayan ta yi sanyi a lokacin azumin watan Ramadan wanda aka kammala a farkon watan Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.