Isa ga babban shafi

An tsige shugaban Majalisar Brazil bisa zargin rashawa

Sakamakon kuri’ar da ‘yan majalisar wakilai suka kada da gagarumar rinjayi ta goyi bayan tsige shugaban majalisar Eduardo Cunha bisa zargin cin hanci da rashawa.

Yan majalisar wakilan Brazil sun tsige shugaban Majalisar  Eduardo Cunha bisa zargin cin hanci.
Yan majalisar wakilan Brazil sun tsige shugaban Majalisar Eduardo Cunha bisa zargin cin hanci. REUTERS/Adriano Machado
Talla

Tuni dai Mr Eduardo Cunha ya danganta tsige shi a matsayin bita da kulli daga bangaren masu biyayya ga tsohuwar shugaba Dilma Rousseff inda ya musanta zargin karbar rashawa na Miliyoyin daloli daga kanfanin mai na Petrobas.

Cunha dai ya taka muhinmiyyar rawa wajen ganin an tsige tsohuwar Shugabar kasa Dilma Rousseff.

Mr Cunha zai gurfana gaban sha’ria akwai kuma yiyuwar tsare shi ganin sakamakon kuri’ar da ‘yan majalisar suka kada ya cire mashi rigar kariya daga gurfana a gaban kuliya.

Mr Cunha dai ya jagoranci tsige tsohuwar shugabar kasar, mace ta farko da ta taba rike mukamin bayan zarginta da laifin cin hanci da rashawa da kuma yin almundahana da kudadden gwamnati zargin da Rousseff ta musanta, ta kuma danganta tsigeta a matsayin juyin mulki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.