Brazil : An amince a tsige Rousseff a Majalisar Dattijai
Kwamitin da Majalisar Dattijan Brazail ta kafa domin nazari akan makomar shugabancin Dilma Rousseff ya amince a tsige shugabar da aka dakatar. ‘Yan majalisa 14 suka amince a kwamitin mai mambobi 19.
Wallafawa ranar:
Wannan matakin dai babbar baraka ce ga Rousseff, wanda zai kawo karshen faduwar gwamnatinta.
Ana zargin shugabar ne da kashe kudade ba bisa ka’idar doka ba tare karbar bashin bankuna a lokacin yakin neman zabe domin fadada ayyukan gwamnati a kasafin kudi.
Tuni dai aka nada babban mai adawa da ita Michel Temer a matsayin shugaban riko, kuma idan har aka tsige ta zai kasance shugaban Brazil har lokacin da za a yi zabe a 2018.
Wannan na zuwa ne a yayin da Brazil ke shirin bude wasannin Olympics a Rio.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu