Afghanistan ta cimma yarjejeniya da 'yan ta'adda
Gwamnatin Afghanistan ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar mayakan da ke karkahsin Gulbuddin Kekmatyr, abin da ake ganin zai ba shi damar sake dawowa fagen siyasar kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tsohon Firaministan kasar Gulbuddin Hekmatyarne ya taka muhimmiyar rawa a lokacin yaki da mamayar Soviet a shekarar 1980.
Bayan wannan yakin ne, arangama tsakanin kungiyarsa da ta Taliban ta tilasta masa tserewa daga kasar, in da shi da mayakansa suka ci gaba da kai munannan hare-hare a cikin kasar, yayin da Amurka ta sanya sunansa a jerin wadanda take nema ruwa a jallo.
Sai dai bayan cimma wannan yarjejeniyar zaman lafiyar, gwamnatin Afghanistan ta amince ta yafe wa Gulbuddin duk laifukan da ya aikata a baya na kaddamar da munannan hare-haren ta’addancin da ya yi sanadiyar rayukan daruruwan mutane.
Tun bayan zaben shugaba Ashraf Ghani, al’ummar kasar ke sa ran ganin ya samar da tsaro ta hanyar tattaunawa da kungiyoyi irinsu Hezb-e Islami masu tayar da kayar baya.
Duk da cimma wannan matsaya dai, masharhanta na ci gaba da bayyana shakku dangane da tasirin wannan yarjejeniya wajen samar da tsaro ga jama'a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu