Isa ga babban shafi
Syria

Faransa ta ce babu dalilin ci gaba da kai hari Aleppo

Ministan Harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault ya shaidawa Rasha cewar babu dalilin ci gaba da kai hare haren sama Aleppo wadanda ke hallaka fararen hula.Wannan ya biyo bayan yunkurin da Faransa ta dauka na farfado da yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria.

Ministan Harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault
Ministan Harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault KENA BETANCUR / AFP
Talla

A ganawar da suka yi a Moscow, Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault ya shaidawa takwaran sa Sergei Lavrov cewar babu dalilin ci gaba da kai hare hare kan fararen hular da ke bukatar agajin gaggawa dan tsira da rayukan su.

Minsitan ya ce ya shaidawa Lavrov gaba da gaba cewar babu wanda zai amince da abinda ke faruwa a Aleppo, inda ya bukaci Rasha ta goyi bayan shirin Faransa na tsagaita wuta.

Takun saka tsakanin Rasha da kasashen Yammacin duniya ya haifar da katsewar yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla dan ba da damar kai kayan agaji ga dubban mabukatan da rikicin ya ritsa da su a Aleppo.

Yau ake saran Ayrault zai kama hanyar zuwa Amurka dan ganawa da John Kerry da kuma gabatar masa da sabon shirin na Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.