Isa ga babban shafi
Syria

Jiragen yaki sun sake yin barin wuta a Aleppo

jiragen yaki sun yi luguden wuta a birnin Aleppo dake cigaba da kasancewa a hannun ‘yan tawaye Syria, tawagar likitoci dake aikin sa kai a kasar sunce harin ya shafi wani babban asibiti ba tare da yin karin bayani ba.

An samu asarar rayukan mutane fiye da dari hudu a birnin Aleppo a mako guda inji MDD.
An samu asarar rayukan mutane fiye da dari hudu a birnin Aleppo a mako guda inji MDD. REUTERS/Sultan Kitaz
Talla

Wannan dai shine karo na biyu da ake kai hari makamancin hakan a birnin na Aleppo a ‘yan kwanakin nan.

Rahotan Majalisar Dinkin Duniya na cewa mutane akalla dari hudu ne suka mutu a mako guda cikinsu har da yara kanana an kuma daura alhakin hare-haren akan dakarun Rasha dana bangaren gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad.

Shekaru fiye da biyar kenan da barkewar yaki a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.