Isa ga babban shafi
Iraq

Mayakan IS sun sace dubban mutane daga kauyukan Mosul

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mayakan IS sun sace dubban fararen hula wadanda ke zaune a kauyukan kusa da birnin Mosul.

Sojojin Iraqi yayin da suka tunkari kudancin birnin Mosul.
Sojojin Iraqi yayin da suka tunkari kudancin birnin Mosul. Reuters/Stringer
Talla

Majalisar ta kara da cewa, sakamakon kin biyayya gare su, mayakan na IS, sun yiwa wasu tsaffin jami’an tsaron Iraqi su 190 kisan gilla tare da wasu fararen hula 42.

A gefe guda kuma har yanzu dai sojin Iraqi da hadin gwiwar mayakan Kurdawa na cigaba da gwabza fada da mayakan na IS, a kokarinsu dannawa cikin birnin na Mosul.

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fargabar cewa, mayakan IS za suyi garkuwa da sauran fararen hula 1,500,000 da suka rage a cikin birnin Mosul, muddin aka dada matsar birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.