Isa ga babban shafi
Iraqi

Dakarun Iraqi suna dab da shiga Mosul

Dakarun Iraqi na dab da shiga garin Mosul bayan shafe kwanaki suna gwabza fada da mayakan IS da suka kwace ikon garin tsawon shekaru biyu. Turkiya ta ce idan an kammala da Mosul tana son a kaddamar da yaki a Raqa na Syria da ke karkashin ikon IS.

Dakarun Iraqi sun kusan shiga Mosul domin kwato garin da ke hannun IS
Dakarun Iraqi sun kusan shiga Mosul domin kwato garin da ke hannun IS REUTERS
Talla

Babban kwamandan da ke jagorantar dakarun Iraqi domin kwato garin Mosul Laftanal Kanal Muntadhar al-Shimmari ya ce kadan ya rage su shiga Mosul.

Kwamandan ya ce mita 700 ya rage, amma wasu rahotanni sun ce mayakan IS sun yi wa dakarun luguden wuta a garin Bartalla da ke gabas da Mosul.
Wani kanal na sojan Iraqi Mustapha al Obaidi an ji yana fadi a rediyo cewa suna kusa da Bazwaya, inda ya ke cewa mayakan IS sun gudu suna komawa cikin garin Mosul.

Sai dai kuma dakarun na Iraqi sun musanta rahotannin da ke cewe sun shiga yankin al Karama da ke cikin Mosul inda suka ce suna dai tsakanin nisan kilomita kimanin 2.5

Ana dai sa ran dakarun Iraqi za su yi wa garin Mosul kawanya amma za su bude kofa ga miliyoyan fararen hula domin su fice kafin su shiga yaki gadan gadan da mayakan IS da suka kwace ikon garin tsawon shekaru biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.