Isa ga babban shafi
Japan-India

Japan zata saidawa India fasahar inganta makamashin Nukiliya

Kasar Japan ta amince ta sayarwa kasar India kayan kafa tashar nukilya hadi da fasahar inganta makamashin Uranium, bayan yarjejeniyar da suka cimma.

Firaminstan India Narendra Modi da takwaransa na Japan Shinzo Abe a birnin Tokyo
Firaminstan India Narendra Modi da takwaransa na Japan Shinzo Abe a birnin Tokyo REUTERS/Franck Robichon/Pool
Talla

Firaministan Japan Shinzo Abe da twakwaransa na India Narendra Modi, sun kuma amince da karfafa alakar tsaro da kasuwanci yayin tattaunawar da suka yi.

Duk da cewa yarjejeniyar bata kunshi bawa India damar kera makamin nukuliya ba, masu sharhi kan tsaro na fargabar maiyiwuwa labari ya canza nan gaba, kasancewar India, bata rattaba hannu kan yarjejeniyar haramta makaman nukililya ba da aka cimma da wasu kasashen Duniya.

Sai dai kuma Shinzo Abe da Narendra Modi sun ce, an cimma yarjejeniyar ce kawai domin cigaban fasaha da zaman lafiya ba domin kera makamin nukiliya ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.