Isa ga babban shafi
Iraqi

An kai wa ‘Yan Shi’a harin bom a Afghanistan

Wani Mumunar harin ta’addanci da kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa ya lakume rayukan akalla mutane 27 a Masallacin Shi’a da ke Kabul a Afghanistan tare da jikkata wasu 64 a lokacin da suke bikin ranar Arba’in ta tuna mutuwar Imam Hussian.

An kai wa 'Yan shi'a harin kunar bakin wake a Masallaci a Kabul
An kai wa 'Yan shi'a harin kunar bakin wake a Masallaci a Kabul REUTERS
Talla

A cewar ‘yan sandan Afghanistan, maharin ya saje ne cikin masu ibada a cikin masallacin na Baqirul Olum da ke yammacin kasar ya tayar da bom.

A kasar Iraqi, Miliyoyan mabiya Shi’a ne suka yi tururuwa suna bugun kirji domin gudanar hajjin Arba’in a birnin Karbala, hajjin da ake gudanarwa bayan kwanaki 40 da Ashura domin jimamin mutuwar jikan Manzon Allah Imam Hossain.

Sai dai ‘Yan shi’ar na hajjin ne cikin tsauraran matakan tsaro saboda barazanar hare haren mayakan IS a Iraqi.

Hajjin Arba’in din ta fado ne yau Litinin da miliyoyan mabiya shi’a ke gudanarwa cikin tsauraran tsaro a Karbala.

Gangamin mahajjatan ya kunshi mabiya da dama daga sassan Iraqi da Iran da Syria.

Labarin da wata jaridar Saudiya ta wallafa mai suna Asharq al-Awsat ya mamaye bikin inda ta yi zargin cewa Iraniyawa na musgunawa mata a lokacin gangamin hajjin na ‘yan shi’a.

Zargin da Firaministan Iraqi Haidar al Abdadi da manyan malaman shi’a suka bukaci Saudiya ta fito ta nemi gafara tare da karyata labarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.