Isa ga babban shafi
Isra'ila

Wutar daji mai karfin gaske ta raba dubban mutane da gidajensu

Dubban ‘yan kasar Isra’ila ne suka tsere daga gidajensu, sakamakon wata mahaukaciyar wutar daji da ta dumfari birnin Hiafa.  

Jami'an kashe gobara da ke fafutukar kashe wutar dajin da ta dumfari birnin Haifa
Jami'an kashe gobara da ke fafutukar kashe wutar dajin da ta dumfari birnin Haifa REUTERS/Baz Ratner
Talla

Hakan ta sa dole rundunar sojin kasar ta bukaci gudunmawar jami’anta da suka yi ritaya, wajen aikin ceto musamman ga wadanda wutar ta ritsa da su a gidajensu.

Magajin Garin birnin na Haifa, Yona Yohav, yace kawo yanzu an samu nasarar kwashe mutane 60,000 daga cikin 250,000 dake garin.

A wani jawabi da ya gabatar, Firaministan kasar Benjamin Netanyahu, yace muddin aka gano cewar da gangan aka hura wutar, za’a dauki wadanda suka aikata a matsayin ‘yan ta’adda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.