Isa ga babban shafi
Koriya ta Kudu

Shugabar Koriya ta kudu za ta yi murabus kafin karshen wa’adinta

Shugabar Kasar Koriya ta Kudu Park Geun-Hye ta ce za ta yi murabus sakamakon tsananin matsin lambar da ta fuskanta daga ‘Yan kasar da suka shafe kwanaki suna zanga-zangar adawa da ita kan zargin cin hanci da rashawa.

Shugabar Koriya ta Kudu Park Geun-Hye
Shugabar Koriya ta Kudu Park Geun-Hye REUTERS/Jeon Heon-Kyun/Pool
Talla

Shugabar ta sanar da haka ne a jawabin da ta yi wa al’ummar kasar inda ta ce a shirye ta ke ta yi murabus kafin cikar wa’adin shugabancinta a 2018.

Amma Shugaba Geun-Hye ta ce za ta mika mulki ga Majilisar kasar wacce za ta tantance makomarta.

Akalla mutane miliyan daya da rabi ne suka gudanar da zanga-zanga a karshen mako inda suka bukaci ganin shugabar ta sauka daga mukaminta ko kuma ganin an tsige ta.

Shugabar na fuskantar zargin badakalar rashawa ne da ita da ta hannun damarta Choi Soon-Sil, da ake tsare da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.