Harin sama ya hallaka fararen hula 100 a Iraqi
Wani harin sama da sojojin gwamnatin Iraqi suka kaddamar a garin Al Qaim da ke yammacin kasar, ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula sama da 100 da jikkata wasu da dama.
Wallafawa ranar:
Bayanai sun nuna cewar an kai harin ne da rana, a lokacin da 'yan fansho ke layin karbar kudadensu, yayin da kuma ma’aikata ke karbar albashi, baya ga hada-hadar kasuwanci da al'umma ke yi.
Shugaban Majalisar kasar, Salim al Juburi wanda ya yi Allah-wadai da harin, ya bukaci kaddamar da bincike kan yadda aka kai hari kan fararen hular cikin kuskure.
Cikin wadanda aka kashe har da yara kanana 19 da mata 12.
To sai dai dakarun da ke yaki da mayakan IS sun musunta kai farmaki a dai dai lokacin da lamarin ya faru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu