Isa ga babban shafi
Iraqi

Mutane 40 sun mutu wurin biki a Falluja

Mutane 40 suka rasa rayukansu, wasu 60 suka samu munanan raunuka a yankin Amiriyat al-Falluja dake kudancin birnin Falluja na Iraqi, bayan jerin hare-haren kunar bakin wake da aka kai cikin motoci, kan taron daurin auren wani jami’in dan sanda.

Wurin biki da aka kai harin kunar bakin wake a yankin Amiriyat al-Falluja da ke Iraqi
Wurin biki da aka kai harin kunar bakin wake a yankin Amiriyat al-Falluja da ke Iraqi
Talla

Mafi yawancin mazauna yankin na Amiriyat al-Falluja da ke kudancin garin Falluja, ‘yan Sunni ne, wadanda suka shafe shekaru biyu, suna fafatawa da mayakan ISIL, tare da taimakawa wajen fatattakarsu daga yankin, a watan Yuni da ya gabata.

Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai jami’an tsaro a kasar, sun bayyana tabbacin kungiyar IS ce ta kai harin.

Sama da shekara guda kenan mayakan ISIS suna rasa yankunan da suka mamaye a kasar Iraqi, yayinda a lokaci guda suke fafutukar cigaba rike ragamar iko da birnin Mosul, tungarsu ta karshe a kasar ta Iraqi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.