Isa ga babban shafi
Iraqi

Mutane 42,000 sun guje wa yakin da ake yi a Mosul

Hukumar da ke kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin da ake na kwato Mosul daga hannun mayakan ISIL ya sa mutane dubu Arba’in da biyu kauracewa gidajensu.

Mutane sama da dubu arba'in da biyu ne suka guje wa birnin Mosul don yakin.
Mutane sama da dubu arba'in da biyu ne suka guje wa birnin Mosul don yakin. Hugo Passarello Luna
Talla

Rahoton ya yi gargadin cewa yakin a Mosul na iya raba sama da Miliyan da gidajensu anan gaba.

Hukumar ta IOM da ke kula da bakin haure ko ‘yan ci rani ta ce yakin da dakarun Iraqi dana kurdawa suka kaddamar a sama da wata guda domin kwato garin Mosul daga hannun ISIL, ya raba mutane kusan 42,000 da gidajensu

Hukumar ta yi gargidin cewa nan gaba yakin zai raba sama da miliyan da gidajensu

Wannan adadin dai ya zarce wanda hukumar ta bayar na wadanda take kula da su a sansanonin da aka tanadar kuma ta ce adadin mutanen zai ci gaba da karuwa

Yawancin mutanen da ke kauracewa yakin sun fito ne daga yankin musul amma akwai wadanda suka fito daga wasu kauyuka da ke kusa da garin.

Wasu rahotannin Majalisar Dinkin Duniya sun ce mayakan ISIL sun tattara fararen hula a cikin Mosul wadanda za su yi amfani da su a matsayin garkuwar yaki.

Tun a ranar 17 ga watan Oktoba ne dakarun Iraqi tare da taimakon Amurka suka kaddamar da farmakin kwato garin Mosul daga hannun ISIL.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.