Isa ga babban shafi
Iraq

Fararen hula na cikin wani hali a Mosul

A yayin da dakarun gwamnatin Iraqi ke kokarin karbe birnin Mosul daga hannun mayakan jihadi, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Norway ta gargadi cewa, fiye da fararen hula miliyan guda ne ke cikin hatsari a birnin.

Dakarun Iraqi na kokarin karbe birnin Mosul daga hannun mayakan IS
Dakarun Iraqi na kokarin karbe birnin Mosul daga hannun mayakan IS Reuters
Talla

An dai yi ta jin karar harbe-harben bindiga a kauyen Gogjali da ke kan gabar brnin Mosul a wannan Laraba, yayin da dakarun Iraqi ke ci gaba da dannawa don isa gabar gabashin birnin.

Fiye da makwanni biyu kenan da dakarun suka fara kaddamar da farmaki kan mayakan IS da zimmar karbe Mosul daya shafe shekaru biyu a hannun mayakan.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasar Norway da ke gudanar da aikin agaji a Iraqi, ta gargadi cewa, yakin Mosul na dab da cikawa da mutanen da ba su ji ba su gani ba.

Darektan hukumar a Iraqi, Wolfgang Gressmann ya ce, sun shirya tsaf don tinkarar munanan matsalolin da za su biyo baya sakamakon farmakin Mosul.

Gressmann ya kara da cewa, jama’a a ciki da wajen Mosul sun shafe shekaru biyu da rabi suna rayuwa cikin dari-dari.

Hukuamar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya ta ce, sama da mutane dubu 20 sun kaurace wa Mosul don samun mafaka a wuraren da ke karkashin gwamnati.

Ita kuwa kungiyar agaji ta Save the Children cewa ta yi, fararen hula da suka hada da kananan yara dubu 600 ke cikin tarkon mayakan IS, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akwai yiwuwar mayakan sun yi garkuwa da dubban mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.