Isa ga babban shafi
IRAKI

Dakarun Iraki sun kwace birnin Nimrud daga hannun ISIL

Birnin Nimrud mai dimbin tarihi ya subuce daga hannun mayakan ISIL bayan da dakarun sojin Iraqi suka yi nasarar kwace garin daga hannun mayakan a farmakin da ake ci gaba don karbe ikon birnin Mosul.

Dakarun Iraki sun kafa tutar kasar a birnin Nimrud baya kwace ikon birnin daga ISIL
Dakarun Iraki sun kafa tutar kasar a birnin Nimrud baya kwace ikon birnin daga ISIL REUTERS/Thaier Al-Sudaini
Talla

Birgediya Janar Saad Ibrahim, kwamanadn runduna ta 9 ya sanar da nasarar, inda ya ke cewa tuni suka karbe kauyukan Al Nomaniyah da Al Nimrud.

Nimrud na daya daga cikin tsofin garuruwan Gabas ta Tsakiya da aka kafa tun a karni na 13 kafin zuwan Annabi Isa Alaihis Salam, kuma ya taba zama babban birnin Daular Syria na wancan lokaci inda Sarakunan kasar suka gina manyan gine gine.

Shekaru biyu da suka wuce ne Kungiyar ISIL ta karbe ikon birnin .

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.